31 Janairu 2016 - 16:18
Mutane 45 sun mutu a wasu hare hare a Syria

Wasu hare haren bama bamai da yawa sun halaka mutane akalla 45 sannan kuma ya jikkata wasu fiye da dari daya a gundumar Sayida Zeinab a bayan birnin Damascus a kusa da wuri mafi tsarki a Syria.

Kungiyar IS ta ce ita ta kai hare haren.

Wakilin BBC a wajen ya bayyana ganin gine - ginen da ke cin wuta da kuma konannun motoci.

Ya ce an kai wa wani mazaunin soji hari.Bashar al Jaafari, shugaban tawagar gwamnati a wajen tattaunawar zaman lafiyar da ake yi a Geneva, ya ce harin ya tabbatar da alaka tsakanin yan adawa da yan ta'adda.

Hubbaren Sayida Zeinab dai na tattare da kabarin jikar Annabi Muhammad (SAW).

Haka kuma 'ya ce gaSayyadina  Ali {a.s}.